Jam'iyyar APC ta fara zawarcin babban gwamna a Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya gana da gwamnan jihar Abia, Alex Otti, a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu
  • Ganawar ta su ta gudana ne a gidan gwamnan dake Umuehim Nvosi a ƙaramar hukumar Isiala Ngwa ta Kudu a jihar Abia
  • Rahotanni sun nuna cewa a yayin ganawar ta su, mataimakin kakakin majalisar wakilan ya buƙaci gwamnan ya dawo jam'iyyar APC wacce ya fice kafin ya zama gwamna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Umuahia, jihar Abia - Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya buƙaci gwamnan jihar Abia, Alex Otti, da ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamna Alex Otti ya bar jam’iyyar APC ne kafin zaɓen 2023 a lokacin da ya kasa samun tikitin tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi bayan mutuwar tsohon Minista a Najeriya

Gwamnan mai shekara 59 da haihuwa ya yi takara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Labour Party (LP) inda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Abia na shekarar 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata ziyara da ya kai a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu a gidan gwamnan da ke Umuehim, Nvosi, ƙaramar hukumar Isiala Ngwa ta Kudu, Benjamin Kalu ya gayawa gwamnan cewa har yanzu yana da waje a jam’iyya mai mulki, cewar Igbere tv.

Me Benjamin ya ce kan Gwamna Alex?

Jaridar The Nation ta ambato Benjamin Kalu yana cewa:

"Ba ka cikin jam'iyya ta kuma hakan ya yi min ciwo. Amma ina so ka sani cewa mutanen nan waɗanda su ma jama'a ta ne suna cikin jam'iyyu daban-daban. Mutane ne waɗanda suke son abin da muke yi.""Mafi yawa daga cikinmu nan mambobin tsohuwar jam'iyyar ka ne. Kuma mun yi kewarka. Mutumin kirki kawai ake yin kewa ba na banza ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tuna da ma'aikata bayan ya yi musu karin N10,000 a albashinsu

"Saboda haka mambobin Labour Party ku shiga taitayinku. Idan ba ku sanya mutumin nan farin ciki ba, zai koma gidansa na asali."

Gwamna Alex Otti ya naɗa muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya kaddamar da kwamitin tsaro domin tabbatar da inganta zaman lafiya a jihar.

Mai girma Gwamnan ya kuma yi wasu muhimman naɗe-naɗe da za su taimaka wurin tabbatar da samun tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6fJdya2aZnmKvtrfAnKBmmpGXr6K6jKCumqWelnqiec2aoZ6qma6ubsXAZqKopZFit6K5yLKwmqpdlr2kew%3D%3D